Friday, June 10, 2022
YADDA ZAKA KARE KANKA DAGA HACKERS (3.0)
MUSTAPHA IBRAHIM HARUNAJune 10, 2022https://muradankarni.blogspot.com/2022/05/amfanin-gmail-account-30.html, https://muradankarni.blogspot.com/2022/05/amfanin-gmail-account-40.html
No comments
YADDA ZAKA KARE WHATSAPP DINKA DAGA HACKERS
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Bayan kammala bayani akan kakkarfan matakin tsaro da zakai amfani dashi wajen kare asusun #Facebook dinka wanda shine kololuwa domin babu sama dashi ayanzu, nan ma zanyi bayani akan tsaro mafi inganci da karfi dazakai amfani dashi wajen kare asusunka na #Whatsapp daga #Hackers,
(Two-step verification)
Ga yadda zakayi;
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
1. Bayan kashiga manhajar whatsapp dinka, kadanna wasu digo guda uku bangaren dama daga sama,
2. Saika shiga Settings
3. Saika danna Account
4. Saika shiga Two-step verification,
5. Saika danna Enable
6. Zai nuna maka inda zaka rubuta lambobin sirri (password/pin) guda shida,
7. Saikuma ka kara rubutawa domin tabbatar da manufarka (confirm pin)
8. Saikuma karubuta email dinka wanda dashine za,ai amfani, idan kamanta lambobin sirrin (forget password)
🔚
Shikenan ka kammala.
#Two_step_verification.
#Two_factor_authentication.
©️M.I.HARUNA
YADDA ZAKA KARE KANKA DAGA HACKERS (2.0)
YADDA ZAKA KARE FACEBOOK DINKA DAGA HACKERS
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️
Mafi kololuwar tsaro wanda yafi kowanne, shine (Two-factor authentication)
Akanshi zamuyi bayani.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
1. Dafarko kashiga setting acikin manhajar facebook ko facebook lite,idan kuma browser ce saika shiga setting and privacy.
2. Sannan kashiga password and security
3. Sannan kadanna Use Two-factor authentication
4. Saikuma kashiga Use text message (sms).
5. Sai kasaka numbar wayarka wadda take aiki, saika danna continue.
6. Daga nan zasu tura maka lambobi guda shida(6) domin tabbatar dacewa lambar na aiki saika danna continue.
7. Two-factor authication yafara aiki, daga nan duk idan kayi login a wata wayar ko browser wadda baka taba login aciki ba, wato (unknown browser) to zasu tura maka lambobin tantancewa (verification code) guda takwas (8) idan kasaka sannan accoun din zai bude.
Kaga koda wani yasan password dinka bazai iya shigaba tunda bazai budeba saika saka lambobin da zasu tura maka alokacin wanda suke canzawa duk bayan minti daya.
Muhadu a #WHATSAPP
🔚
©️M.I.HARUNA
YADDA ZAKA KARE KANKA DAGA HACKERS (1.0)
YADDA ZAKA KARE FACEBOOK DINKA DAGA HACKERS. (1.0)
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Kasantuwar samun matasan hackers (upcoming hackers) yasa ake yawaita kutse acikin social media musamman facebook dayake da saukin mu,amala da farin jini,
Wasu daga cikin masu kutse cikin account din mutane, sunayine domin gwada ilimin da suka koya na hacking wato NETWORKING SKILLS wanda yahada da ilimin;
1. WEP versus WPS password
2. NAT
3. MAC Addresses
4. Routers
5. Ports
6. VPN
7. IPv6
8. DNS
9. Subnetting
10. DHCP
11. Private and public IPs
12. Ipv4
13. OSI Modelling
14. Packets
15. TCP/IP
Wasu kuma sunayine domin kasuwanci,
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Sukan duba mutumin da yake da abokai masu yawa domin suyi amfani da account dinsa suke tallace-tallace aciki, kamfanin da sukewa tallar yana biyansu.
Wasu kuma domin su aikata laifi,
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Sukanyi hakanne domin kada akamasu kaikuma kashiga hannu, kaga kataka sawun barawo kenan,shine kutse mafi muni, wani yayi amfani da zatinka ya aikata laifi, azo bincike akamaka bakaci nanin ba nanin tacika Allah ya sawwake.
Wasu kuma sunayine domin suyi damfara,
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Zasuyi amfani da account dinka su rika turawa abokananka sako cewa kana neman taimako ataimaka maka da kudi ko katin kiran waya,
Amatsayin kaine tunda shidai ba ganinka yakeba,kaga bazai gane cewa bakaineba, kaga an zubar maka da mutunci.
Muhadu a fita tagaba domin sanin yadda zaka kare kanka daga yan #dandatsa
🔚
©️M.I.HARUNA
Recent Post
WHAT'S THE WEAKNESS/STRONGEST OF DXY
Today, February 19, 2026, the US Dollar Index (DXY) is actually displaying short-term strength, trading near a two-week high around the 97....










