Monday, December 26, 2022
MENE NE FASAHAR ARTIFICIAL INTELLIGENCE(A.I)
➡Amincin Allah yatabbata agareku⬅
Ayau idan Allah yaso ya yarda zamuyi bayanine akan Fasahar A.I (artificial intelligence)wato kwaikwayon zubin dabi,ar dan adam.
Duniyar fasaha na kara cigaba, kasancewar kullum bincike akeyi anata kara tsatsubar sababbin fasahohi,
➡➡➡➡➡➡➡➡➡➡➡➡
Mene ne tsarin fasahar A.I?
tsarin fasahar a.i tsarine da aka sanyawa na,ura mai kwakwalwa domin takeyin tinani dakanta dakuma koyon abu dakanta (marchine learning) batare da ankoya mataba,sannan tana gudanar da abubuwa kamar dan adam ta sigar musayar bayanai,zakuyi hira da ita,zata baka shawara.
Misalan fasahar A.I
1. robot wato sakago; mutummutumi shima ansanya masa wannan fasahar tayadda zakuyi hira dashi kamar ,mutum kuma yanayin tinani sannan zai aiwatar da komai da kansa.
2. manhajar bincike ta GPT(chat.openai) wadda aka kirkira kwanannan da ta kerewa manhajar bincike ta google saboda ita zata baka amsane kai tsaye amma google zata baka inda akai rubutu akan abinda yashafi tambayarka ne,
3.Self driving car (mota mai tuka kanta) kawai saidai ka leka kaga steering na juyawa amma babu kowa aciki,ansanya mata tsarin tasan cewa tashiga cunkoso ko kuma ita kadai ke tafiya zata gane cewa tazo traffic ta tsaya idan kuma tabada hannu tagane ta tafi,
4. Manhajar da zata taimaka maka wajen wasu ayyukan na yau da kullum kamar kasuwanci,ta lissafa maka adadin kayan daka sayar da ribar daka ci da sauran wasu ayyukan daka sa taimaka,
5. Gida mai gudanar da kanshi ; wanna gida da abin mamakin yake domin idan kadawo daga wajen aiki ko kasuwa zaka shiga magana kawai zakaimasa yabude kaiwa bulb magana yakawo haske,kakira abinci daga kitchen yazo dining.
↘↘↘↘↘↘↘↘↘↘⬇↘
Rabe-Raben Fasahar A.I
⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
1.Artificial Intelligence (AI) ― wannan nau'i yana bayani akan shi din kansa fasahar (AI), watau fasahar na'urar mai kwakwalwa wacce aka ginata abisa son ta kwaikwayi ayyukan da kwakwalwar Dan-Adam take yi watau ‘Dabi'a’ kamar tunani, nazari, da sauransu.
2. Artificial General Intelligence (AGI) wannan kuma so ake AGI ya kasance ya fi AI ta yadda za'a daidaita fasahar da yin abu sak irin na Dan-Adam, watau duk wani abun da mutum zai iya yi na dabi'arsa - to fasahar AGI zata iya yi.
3. Artificial Super Intelligence (ASI) ― Wannan nau'i mai abun mamaki kenan. Watau ita fa wannan so ake ta ma fi Dan-Adam din; so ake ta fi Dan-Adam duk wasu dabi'u da ka san Dan-Adam yana da su. Ana son ne ta yiwa Dan-Adam fintinkau a komai.
Sannu akan hankali zamu zo wajen.
©M.I.HARUNA
Recent Post
WHAT'S THE WEAKNESS/STRONGEST OF DXY
Today, February 19, 2026, the US Dollar Index (DXY) is actually displaying short-term strength, trading near a two-week high around the 97....










