Cigaba...
A darasin daya gabata munyi bayani akan menene Gmail da kuma amfaninsa,to yanzu zamu cigaba;
- DUO: wata manhaja ce wadda kamfanin google suka gina saboda yin (video call) Wato yin kira kana ganin mutum yana ganin ka, domin cin moriyar hakan saika sauke Manhajar a rumbun manhajoji na google wato playstore, Kabude kayi register da lambar wayar ka, duk wanda yayi register acikin lambobin wayarka zaku hadu, haka zalika idan kasaka gmail dinka acikin computer tahanyar manhjar lilo-lilo ta chrome zaka iya video call da mutum wanda yake acikin contact dinka matukar yana online, zaka gane haka ne idan kaduba hagu daga kasa an rubuta chat idanka taba wajan zainuna maka wanda yake online da koriyar alama.
- COMPOSE MAIL: Kirkirar sako ko wasika dan turawa wani ko adanawa dan gaba, Kaduba sama daga hagu idan kadanna zai nuna maka wajan rubuta wasika, To: yana nufin wanda zaka turawa sakon, zaka iya rubutawa kuma zaka iya dakkowa cikin wadanda kake dasu daya ko sama da haka, amma idan sunfi daya zakake raba tsakanin su da comma ( , ) misali; miharuna3449@gmail.com,sulphuricacid3449@yahoo.com haka zakai konawa ne. MESSAGE: yana nufin sakon da zaka tura wato (message body), ATTACHEMENT: wato hada sakon da wani file, hoto ko documents, sai kuma SEND wato tura sakon kenan.
- MEETING: Ganawa tsakanin wasu mutane domin tattauna wasu muhimman batutuwa,a kamfani ko makaranta da sauran wurare, idan kashiga gmail ta manhajar lilo-lilo ta chrome kasa daga hagu zakaga an rubuta #meeting idan kadanna zai baka zabi biyu kodai ka kirkiri ganawar(meeting) kokuma ka amsa gayyatar ganawar ta hanyar rubuta wasu lambobin sirri da makirkirin ganawar yabaka.






0 comments:
Post a Comment