BARKA DA ZUWA MAKARANTAR KOYON COMPUTER ACIKIN HARSHEN HAUSA DA KUMA YADDA FASAHA TAKE GUDANA ACIKIN DUNIYAR INTERNET. karka manta da following comment dakuma tambaya.

HOME

Friday, February 26, 2021

YADDA ZAKA KARANTA PDF FILE CIKIN SAUKI DA WAYAR JAVA.

 Java Phone Yanda Zaka Karanta PDF File Cikin Wayoyin Java

Wata Babbar matsala Da Masu Wayoyin Java Ke Fuskanta Itace Wajen Bude PDF File, A Cikin Wayoyin Nasu. Wasu Ma Kan Iya Nazari Akan Hakan Zai Yiwu makuwa,Menene PDF File Abunda PDF Ke Nufi Shine, PDF File A Turance Yana Nufin [Fordable Document Format] Shi PDF File Shine File Da Zaka Iya Kiransa Da Littafi Da Ake Karantashi Cikin Wayoyi Da kwafumtoci Yana Da Extension (.pdf), Wato Karshen File Din Yakan Karene Da .pdf . Kamar Ire-Iren Wayoyin Android dasuke zuwa da pdf reader da kuma applications softwares wato wadanda ake downloading dinsu a rumbunan manhaja, irinsu googleplaystore.com da amazonstore.com appsstore.com apkpure.com dasauransu,
haka zalika itama java nada nata apps din wanda ake kira bluetooth file transfer (blueftp) kuyi seaching nashi a google.com kusaukeshi bayan kun kammala saiku budeshi, zai nemi kabude bluetooth din wayarka idan kaso zaka iya budewa koka kyaleshi kazabi memory bayan yabude zainuna maka foldodi kamar haka:-
  1. (root)
  2. phone(c:)
  3. memory card (E:) saika shiga inda ka ajiye pdf din; idan kaje wajen budeshi saika danna menu zakaga(open as text) saiaka danna shi shikenan zakaga yabude.
Share:

Thursday, February 25, 2021

YADDA AKE HADA CCTV CAMERA CIKIN SAUKI

YADDA ZAKA HADA CCTV CAMERA DA WAYARKA TA ANDROID
Yadda ake hada cctv camera da wayarka ta android, kamar dai yadda muka sani cctv kyamara ce ta tsaro da ake amfani da ita a ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu saboda tabbatar da tsaro, to kaima zaka iya hada taka acikin dakinka kake ganin meke gudana acikin farfajiyar gidanku batare daka kashe kudiba, idan dakinka acikin gidanku yake, idan kuma a ajihun zaure kake kwana kuma to saikai sa'ido wa "yan matan dake wucewa ta layinku, ga yadda zakai dafarko dole ne katanadi wayar android guda 2, sannan kajeka google playstore.com kadauko wani application maisuna walkietooth idan kasaukeshi ka girkashi(installing) sannan kabudeshi zakaga zabika (option) kamar haka:-
  1. Voice
  2. Camera
  3. Setting 4.Help
  4. Voice:- idan kanaso kakejin murya kawai banda hoto.
  5. Camera:- idan kanaso kake ganin hoto mai motsi kamar dai yadda cctv take aiki.
  6. Setting:- saitunan manhajar.
  7. Help:- domin sanin yadda ake aiki dashi apps din. To saika zabi camera ko voice yadanganta da irin bukatar ka,amma zamuyi magana ne akan camera, amma duk tsarin dayane idan kazabi camera zai bude kamar haka:-
  8. bluetooth * server * client
  9. wifi-direct * server * client
  10. wifi * server * client
  11. wifi hotspot * server * client 1. Anan zaka iya hadawa tahanyar amfani da bluetooth, yadda akeyi shine manhajar(application) daka sauke zaka tura a daya android din saika zabi wacce ce zata zama uwar-garke (server) wadda zakake kallon meke faruwa ta cikinta kamar kana kallon bidiyo, saikuma kazabi wacce kayadda da kyamarat ta tazamar maka camera(client), a wayar dakake so kake kallon abinda kyamarar take haskawa, saika danna server to bluetooth dinka zaibude ita kuma wadda zata zama camera saika danna client itama blutooth zaibude amma ita searching na bluetooth zakaga tanayi saika jira takammala idan tanemo sunan bluetooth na server saikai taba kan sunan zaifara pairing zakaga tanemi izini daga server saika danna yes shikenan kahada,saika danna hoton camera acikin android din damukace kadanna client yayin hadawa zakaga hoton abinda take haskawa, itakuma android dinda mukace kadanna server yayin hadawa zata fara amsar sakon hoto mai motsi wato zakake ganin duk wani abinda kyamarar daya android dinnan take haskawa,saika ajiye client a inda kake bukata,sannan kanada damar aikawa waccen wayar sako tahanyra wata alama dake kasa mai alamar chat, hakama abin yake idan da wifi zaka hada ko hostpot.
KUKASANCE DAMU
Share:

Tuesday, February 23, 2021

YADDA AKE KIRKIRAR VIRUS

                YANDA AKE KIRKIRAR VIRUS

👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎👎

Assalamu'Alaikum! *Me Ake Bukata Domin Gudanar da Wannan Aikin?* Abinda Ake Bukata shine {Notepad} na cikin computar ka. *TA YAYA ZAN KIRKIRI VIRUS DIN?* 1.kai ka Copy wadannan code din dake a kasa. @echo off :begin msg *Your PC HAS BEEN HACKED BY SOMEONE msg *File will delete by Virus msg *3 msg *2 msg *1 msg *All of Your Files Have Been Deleted GOTO :BEGIN 2. saikaje cikin {Notepad} dinka kayi paste dinsu a ciki, sannan kayi save din wadannan code din da suna kamar haka file.bat [Hattara idan kazo wajen save na file din to kana iya sanya masa sunan da kake bukata ammafa ya kasance kasaka (.bat) akarshen sunan, misali idan sunan daka saka miharuna ne to saikasa miharuna.bat sannan kai saving, to duk computer daka sakawashi kuma kabudeshi to saita hargitse,idan kuma anaso tadawo dai-dai sai ayi rebooting nata ko restart.

Share:

DARASI NA FARKO (1)

 

ASSALAMU ALAIKUM

MENENE COMPUTER

Menene COMPUTER kalmar computer tasamo asaline daga kalmar compute wato (lissafawa),

Kwamfuta nanufin duk wata na`ura da zata taimaka maka ka gabatar da wani aiki

Kwamfuta a gundarin harshen hausa na nufin na`ura mai kwakwalwa.

 

ABUBUWANDA KWAMFUTA TA KUNSA

 

 

             


 

JIGA-JIGAN AYYUKAN DA KWAMFUTA TAKEYI

 Karbar kunshin bayanai wato (data)

Sanya mata kunshin bayanai (data)

 Sarrafa bayanai

  Sarrafawa

 Fitar da  bayanai

  Fitar da sakamako

 Adana saka mako

  Ma`ajiya

1 1.    Input data (saka danyan bayani)

Input data na nufin sanyawa kwamfuta danyan bayani ta siffar lambobi,bakake hotuna,bidiyo, sauti dasauransu, ta hanyar amfani da na`urar mashigar da danyan bayani(input device).

2 2           Process data: (sarrafa danyan bayani)

Processing data na nufin sarrafa danyan bayani da na`ura keyi yadda aka tsara mata,kuma hakan nafaruwa ne acikinta ma,ana ba,a iya ganin lokacinda hakan ke faruwa

3 3.       Output: (fitar da sarrafaffun bayanai)

Output nanufin fitar da sarrafaffun bayanai da na`ura takeyi yayin da ta kammala sarrafasu zata baka su amatsayin sakamako.kuma ana adanashi ne acikin ma`adana wato (storage device).

ALHAMDU LILLAH NANNE KARSHEN DARASI NA FARKO SAIKUMA HADUWA TA GABA,IDAN AKWAI MAI TAMBAYA YA IYA YINTA.

Share:

Tuesday, February 9, 2021

YANDA AKE DAWO DA KAYAN DA SUKA BACE A MEMORY

YADDA AKE DAWO DA KAYAN DASUKE KAN MEMORY BAYAN AN GOGESU. DAGA FASAHAR COMPUTER. Daya daga cikin tambayoyin dajama’a suke yi a kowanelokaci shi ne ya mutum zai yi al-kacindayarasa kayan da yaajiye a cikin memory SD Card nawayarsa, Camera a sanadiyar kankare memory (formatting) kokuma an goge abin da ke ciki (deleting). Amma kafin in fadi yadda ake yin wannan aiki ko kuma manhajoji (software) da ake bukata yana da kyau in sanar da jama’a yadda shi wannan memory yake da kuma yadda ake lura da shi. Memory dai wani irin mazubi ne da aka yi shi domin ya ba mutum damar ya iya yin ajiyar kayan da aka yi su da wutar lantarki (electronic data) wanda ya hada da hotuna da rubutu da surkulle da duk wani abu da ake iya adana shi a cikin computer. Wadannan memory yana da yanayi mabanbanta dangane da yadda ake yin sa da kuma tsarin yinsa, sai dai mafi shahara shine wanda ake yin amfani da shi amafi yawan wayoyin tafida gidanka na zamani. A baya, mafi yawan kanfanonin dasuke kirkirar wayoyi ko kamara kowa na yin irin nasa memory, dangane da girma ko fadi, wanda ya sanya akwai matsalasosai yadda memorin wani kamfani baya aiki a wata na’ura da ba tasa ba. Amma bayan da waya kirar Android ta samu karbuwa sosai aduniya sai ya zama sun sami hadin kai wurin tabbatar da mazubin memory ya zama yana darami iri daya wanda zaizama kowace waya ko tablet zata yi amfani da su. A baya wannan memory ya na da tsada matuka, ga shi kuma yana da wahalar samuwa a kasash-en mu, ga shi kuma ba shi da girman wurin kwasan bayanai, amma Alhamudu Lillahi a yanzu wannan ta kau domin ana samu memory wanda a kalla yana iya daukar Gig dubu shi kadai. Daga cikin abin da yake damun jama’a shi ne yawan lalacewarsa da kuma rashin sa’a wuringogewar abin da ke ciki. Mutane da dama suna manta cewar Memory shima kayan kwam-futa ne, kuma yana iya lalacewa kowane lokaci, musamman idan aka yi rashin sa’awanda yake rike da shi bai iya lura da shi. Wani lokaci ba wai memorin ya lalaceba ne, a a an sami matsala ne da inda aka saka shi. Misali zai iya yuwuwa ka sami wayar da take daukar memory dayake da tsarin ajiyar bayanaina FAT (File Allocated Table) to idanka saka shi a cikin wata wayar da baya daukar wannan tsarin sai ka ji ta fada maka cewar wannan memorin yayi dameji. Ko kuma wani lokaci zaka ga duk abin da ke cikn memorin ya ki budewa ko kuma ya nuna alamar lalacewa wanda wannan shima ba yana nuna cewar memorin ya daina aiki ba ne kokuma kayan cikinsa sun lalace. Shima wannan yana dadanganta ne da irin File Sysmem din da aka ajiye kayan tunfarko. Wani lokaci kuma zaka ga ka dauko kaya daga cikin kwamfuta ko wata wayar amma da zarar ka tashi budewa sai ka ji ya nafada maka cewar Unsupported format wannan shima ba yana nu-fin cewar memorin ya lalace ba ne yana maganar cewar wayar bata da application din da zai bude. To duk wadannan ba abin da za mu yi magana ba ne a kai. Muna son muyi magana ne ga mu-tum da cikin rashin sani ko ma ganganci ya goge abin da ke cikin memory na wayarsa kuma yana son ya sake dawo da wannan kaya. A tsari irin na bature da kuma yadda yayi kayan ajiya na kwamfuta wato storage devices yana da kyau jama’a su sani cewar duk abin da ya taba shiga cikin memory na kwamfuta kowaya ko flash har abada yana nan, koda kuma an goge shi ko an yi formatin lallai yana nan, kumaza a iya dawo da shi. Saidai inda gizo ke saka shi ne dame yakamata in yi amfani wurindawo da wadannan kayan? Akwai hanyoyi mabanbanta da jama’a suke yin amfani da su wurin dawo da kayan da suke ci-kin memory, kadan daga ciki shine ta yin amfani da shafukan intanet domin samun biyan bukata. Sai dai a nawa shawarar ban cika son jama’a suna yin amfani da wasu shafukan intanet wurin irin wannan aiki ba, kasancewar mafi yawan irin wadannan shafuka na yan yaudara ne da zam-ba da kuma zubawa mutane miyagun virus cikin wayarka ko kuma kwamfutar ka. Amma akwai na kirki saidai mafi yawansu sai ka biya kudi. A wannan karatun zan nuna mana wadansu manhajojin kwamfuta na kyauta kuma garanti gaduk wanda yake son yayi amfani da su wurin dawo da kayan dasuka bace a memorinsa. Idan memorin yana cikin waya ne kokuma cikin kamara kuma idan ka hada shi da kwamfuta baya nuna memorin to yana dakyau ka ciro memorin daga cikin inda ya ke ka saka shi a cikinCard Reader domin fara yin wannan aiki. Abin kiyayewa shi ne, tunda dakwamfuta zaka yi wannan gyara to ka sani mafi yawan kwam-futar da muke amfani da ita a wannan kasa ta mu kashi 60 suna dauke da virus mai cinye kayan kwamfita ma mayar da su shortcut, to, amfani da irin wannan kwamfutar akwai hatsari, saboda haka ka sami kwamfutar da ka san tana da anti-virus mai kyau, kuma ana updating dinsa kafin ka zura shi. Wani hanzari ba gudu ba, idan kasan akwai wadansu kaya acikin memori din to yana da kyau ka kwashe su ka zuba su acikin wani folder domin kada garin so ka dawo da baya ya zama suna da suna iri daya da wannan sai ya daura a kansa. Wadannan dai sune kadan daga cikin abin da zan iya janhankali a kai kafin in nuna mana soft-ware din da zan yimagana a kai. Amfani da wadannan application ba wani wahala ya ke da su ba, da farko dai dukkansu kyauta ne kuma suna yin aiki sai kamar yadda ya kamata duk da de ba wai zan fadi mataki bayan mataki bin kowane daya daga cikin su ba ne, sai dai zan fadi shi application din dakuma amfanin sa.1 Recuva (Na aiki a Windows ne kawai) Wannan applica-tion na Recuva(version 1.5) nauyin sa 4.02MB ne kuma kyauta ne, yana aiki a kwamfutar da take da operating system na Windows ana kuma iya saka shi a Windows 2000 zuwa sama. Idan kana son ka dawo da files din ka dake cikin memory din ka. Zaka saka memorin a cikin Card Reader sannan ka zura shi a cikin kwamfutar da ka yi installing wannan application na Recuva, sai ka tashe shi (recuva) sai ka zabi shi memori din acikin jerin manyan kwakwalen da suke jikin kwamfutar. Sannansai ka taba maballin Scan.Zaka bashi lokaci don zai dawo dakayan da aka goge a cikinsannan zai baka maballin da aka rubuta Recover sai ka taba shi domin ya dawo maka da wanda kakeso.2 Pando-ra Recovery (Na aiki a Windows ne kawai)Pandora Recovery shi ma kyauta ne yana da girman 3.12MB,yana aiki a kwamfutar da aka sa mata Windows kuma wacce Operating System dinta ya fara da Windows XP zuwa sama. Shima yana aiki ne kamar yadda recuva, wato za a ciro memorin a saka a cikin Card Reader sai a saka a cikin kwamfutar da akayi Installing Pandora Recovery.Sannan zai zabi kodai yayiQuick Scan ko Deep Scan. Shi na Quick Scan ga wanda ya keson ya dawo da abubuwan ya-yi deleting ne amma wanda yake son ya dawo da wadanda aka yi formatting shi zai amfani da Deep Scan.Bayan ya gama scanning za ka iyazaba tsakanin kodai ka yi amfani da Pandora Re-covery Wizard sai ka yi amfani da sharudda da zai rika fitowa kana zaba har ka gama, ko kuma ka yi right click ka zabi abin da kake son ka dawo da su. This post is copyright from fasahar internet 'kimiyya'
Share:

KASUWANCIN YANAR GIZO-GIZO

HADA HADAR KUDADE TA CRYPTOCURRENCY Wani Sabon Kamfani JAAlifestyle Daga England, Ya Baje Manhajarsa A Nigeria Domin Samun Kudi Ta Online Kyauta. JAAlifestyle ko baka saka kudinka ba idan har kayi rajista zaka samu kudi cikin hanya mai sauki, kayi ragista https://secure.jaalifestyle.com/ref/zaharaddeengandu JAAlifestyle 'Yan Jaridu suna fira da wakilansu a jihar Katsina, a gidan radiyo na Vision FM 92.1 da misalin karfe 5:00pm a ranar kowacce Asabar. Sannan Kuma yau sun gabatar da wani taro na wayar dakai a cikin Mumbayya House Kano, Sa'adu Zungur hall, da misalin karfe 11:00am. Wannan shi ne kadan daga cikin hanyar da zaka binciko gaskiyar kamfanin JAAlifestyle, lokacine da Allah ya kawomu ta yadda zamu samu rufin asiri cikin sauki na rayuwa, kuma yakamata ku sani cewa; wannan ba kamar irin sauran da kuka Sani bane, irinsu; INSME, U-WORK, GET APP, MY BONUS da sauransu. Wannan Gwamnati tasan da shi, kuma manyan kasar sunsan da shi, kuma ansan kowa tinda zaka iya zuwa wajen wakilansu, Sannan Kuma ko baka saka kudinka ba zaka iya samun kudi duk wata kuma ka fitar da zarar ya fara aiki, Wallahi ku jaraba kuyi rajista. https://secure.jaalifestyle.com/ref/zaharaddeengandu JAAlifestyle Kamfani ne mai zaman kanshi Wanda kuma ya hada manyan kasashen duniya da yawa, wanda Allah ya sa muma Muna daga cikinsu, dan haka idan kana buqatar qarin bayani a kan wannan platform din zaka iyayin searching a Google ko Facebook na JAALIFESTYLE domin kasamu karin bayani da gamsuwa fiyeda haka, ko kuma Ku yi joining ta WhatsApp dinsu. https://chat.whatsapp.com/CeqoRyivtM6Ecbkyyj978M
Share:

KASUWANCIN YANAR GIZO-GIZO

KASUWANCIN YANAR GIZO-GIZO Bitcoin shine crypto currency mafi girma a duniya, amma akwai dubbunnan sauran crypto a kasuwa. Yana da amfani ka samu ƙarin sani game da duniyar crypto harma kasan coins ko tokens da za a saya a cikinsu . A cikin wannan rubutun, zaka fahimci nau'ikan nau'ikan cryptocurrencies da yadda zaku iya amfani da wannan ilimin don zaɓar coyinin ko kuma token. Tun zuwan Bitcoin shekaru goma da suka gabata, an ƙirƙiri dubunnan sauran coins da tokens na cryptocurrencies, waɗanda aka haɗa su da suna altcoins, wato alternative coins. Misali, bayanin babban gidan yanar sadarwar na kasuwancin crypto na CoinMarketCap a halin yanzu yana dauke da coins 8,350, tare da yiwuwar dubunnai masu zuwa nan gaba. akwai coins da suke kan tsarin fasahar blockchain kamar, Ethereum (ETH) shine babban coins dayake kan fasahar blockchain na biyu a duniya bayan Bitcoin. Izuwa yanzu akwai tokens sama da 280,000 a kan hanyar Blockchain network na Ethereum wato ERC-20, kuma sama da 40 daga cikin waɗannan tokens suna cikin manyan cryptocurrencies 100 a duniya a kasuwar coin market cap. Ethereum yayi nisa sossai a tsarin a blockchain, a yanzu haka, akwai biyu daga cikin coins da ake gani a matsayin abokan hamayyar Ethereum, sune Polkadot (DOT) da Cardano (ADA), a halin yanzu sune na hudu da na shida mafi girma a duniya. Polkadot ya nada fasahar blockchain na musamman inda yake hada blocks dayawa kuma ya dunkule su a cikin hanyar network guda ɗaya, yayin da Cardano babban maƙasudin blockchain ne wanda ke alfahari da kasancewa bisa ga binciken masana na ƙwararru wato research. Sauran nau ikan crypto waɗanda galibi suke ƙarƙashin wannan rukunin sun haɗa da Tezos (XTZ), EOS (EOS), da Tron (TRON) da ma sauransu. a cikin duniyar crypto, akwai ra'ayoyi da yawa, da tunani game da abin da zai zamo madadin Bitcoin, wannan yasa aketa kirkiran coins da tokens.. Bisa ga adalci, zamu guji bada takamaiman wane coins zaka siya domin ita ribar na iya zuwa cikin kankani ko kuma dogon lokaci wanda bamu da tabbacin fada maka ga lokacin, amman anamu bangaren akwai wanda muke musu kyakkyawan zato nan gaba, domin zasu kawo alheri sossai, aƙalla a yanzu zaka ga rukunonin kala kala na coins da tokens da masana'antun suke kirkira a yan shekarunnan wanda amfani dasu daza ayi dasu wurin kasuwancin, siye ko kuma siyarwa shi zai ba coins nasu daraja a kasuwa, a haka dai suke tunanin zasu zarce bitcoins. A ƙarshe, muna ƙarfafa cewa duk kudin da zaku saka akan crypto kar ya zamo kuɗin da kuke bukatar su nan kusa, kuma akarshe ka tuna ba saka jari kayi ba, kadara kasiya ka ajiye zuwa wani lokacin in farashinta yatashi zaka siyar haka zalika wannan kadarar taka farashin zai iya faduwa, zaka iya siyarwa nan take ko kuma kajira har sai darajar ta a kasuwa ya tashi ma'ana kayi haquri har ya koma yanda yake sannan kasiyar, zabi ya rage ga naka . Mu a Kamfanin Fafutuka mun yarda da 'yancin kuɗi' domin kai kasan nawa kake da halin sakawa a wannan harkar, karku manta duk kasuwancin da mutum zaiyi akwai riba da faduwa, toh hakama a crypto akan fadi shima. Mun aminta cewa zai fi kyau mu taimaka mu sanar da ku game da abin da ake kira “crypto” Ya zaku siya, kuma ya zaku siyar, a kyauta zamu koya muku in kun zo ofishin mu. Sannan mu ba ku kwarin gwiwar yin bincike da kanku, da kuma yanke shawarar mai yakamata kuyi. this post is copyright.
Share:

Recent Post

WHAT'S THE WEAKNESS/STRONGEST OF DXY

 Today, February 19, 2026, the US Dollar Index (DXY) is actually displaying short-term strength, trading near a two-week high around the 97....

FOREX TRADING NEWS