Tuesday, February 9, 2021
Home »
» KASUWANCIN YANAR GIZO-GIZO
KASUWANCIN YANAR GIZO-GIZO
KASUWANCIN YANAR GIZO-GIZO
Bitcoin shine crypto currency mafi girma a duniya, amma akwai dubbunnan sauran crypto a kasuwa. Yana da amfani ka samu ƙarin sani game da duniyar crypto harma kasan coins ko tokens da za a saya a cikinsu . A cikin wannan rubutun, zaka fahimci nau'ikan nau'ikan cryptocurrencies da yadda zaku iya amfani da wannan ilimin don zaɓar coyinin ko kuma token.
Tun zuwan Bitcoin shekaru goma da suka gabata, an ƙirƙiri dubunnan sauran coins da tokens na cryptocurrencies, waɗanda aka haɗa su da suna altcoins, wato alternative coins. Misali, bayanin babban gidan yanar sadarwar na kasuwancin crypto na CoinMarketCap a halin yanzu yana dauke da coins 8,350, tare da yiwuwar dubunnai masu zuwa nan gaba. akwai coins da suke kan tsarin fasahar blockchain kamar, Ethereum (ETH) shine babban coins dayake kan fasahar blockchain na biyu a duniya bayan Bitcoin. Izuwa yanzu akwai tokens sama da 280,000 a kan hanyar Blockchain network na Ethereum wato ERC-20, kuma sama da 40 daga cikin waɗannan tokens suna cikin manyan cryptocurrencies 100 a duniya a kasuwar coin market cap.
Ethereum yayi nisa sossai a tsarin a blockchain, a yanzu haka, akwai biyu daga cikin coins da ake gani a matsayin abokan hamayyar Ethereum, sune Polkadot (DOT) da Cardano (ADA), a halin yanzu sune na hudu da na shida mafi girma a duniya.
Polkadot ya nada fasahar blockchain na musamman inda yake hada blocks dayawa kuma ya dunkule su a cikin hanyar network guda ɗaya, yayin da Cardano babban maƙasudin blockchain ne wanda ke alfahari da kasancewa bisa ga binciken masana na ƙwararru wato research. Sauran nau ikan crypto waɗanda galibi suke ƙarƙashin wannan rukunin sun haɗa da Tezos (XTZ), EOS (EOS), da Tron (TRON) da ma sauransu.
a cikin duniyar crypto, akwai ra'ayoyi da yawa, da tunani game da abin da zai zamo madadin Bitcoin, wannan yasa aketa kirkiran coins da tokens..
Bisa ga adalci, zamu guji bada takamaiman wane coins zaka siya domin ita ribar na iya zuwa cikin kankani ko kuma dogon lokaci wanda bamu da tabbacin fada maka ga lokacin, amman anamu bangaren akwai wanda muke musu kyakkyawan zato nan gaba, domin zasu kawo alheri sossai, aƙalla a yanzu zaka ga rukunonin kala kala na coins da tokens da masana'antun suke kirkira a yan shekarunnan wanda amfani dasu daza ayi dasu wurin kasuwancin, siye ko kuma siyarwa shi zai ba coins nasu daraja a kasuwa, a haka dai suke tunanin zasu zarce bitcoins.
A ƙarshe, muna ƙarfafa cewa duk kudin da zaku saka akan crypto kar ya zamo kuɗin da kuke bukatar su nan kusa, kuma akarshe ka tuna ba saka jari kayi ba, kadara kasiya ka ajiye zuwa wani lokacin in farashinta yatashi zaka siyar haka zalika wannan kadarar taka farashin zai iya faduwa, zaka iya siyarwa nan take ko kuma kajira har sai darajar ta a kasuwa ya tashi ma'ana kayi haquri har ya koma yanda yake sannan kasiyar, zabi ya rage ga naka . Mu a Kamfanin Fafutuka mun yarda da 'yancin kuɗi' domin kai kasan nawa kake da halin sakawa a wannan harkar, karku manta duk kasuwancin da mutum zaiyi akwai riba da faduwa, toh hakama a crypto akan fadi shima.
Mun aminta cewa zai fi kyau mu taimaka mu sanar da ku game da abin da ake kira “crypto”
Ya zaku siya, kuma ya zaku siyar, a kyauta zamu koya muku in kun zo ofishin mu.
Sannan mu ba ku kwarin gwiwar yin bincike da kanku, da kuma yanke shawarar mai yakamata kuyi.
this post is copyright.
Recent Post
WHAT'S THE WEAKNESS/STRONGEST OF DXY
Today, February 19, 2026, the US Dollar Index (DXY) is actually displaying short-term strength, trading near a two-week high around the 97....






1 comments:
dakyau
Post a Comment