Tuesday, February 9, 2021
Home »
» YANDA AKE DAWO DA KAYAN DA SUKA BACE A MEMORY
YANDA AKE DAWO DA KAYAN DA SUKA BACE A MEMORY
YADDA AKE DAWO DA KAYAN DASUKE KAN MEMORY BAYAN AN GOGESU.
DAGA FASAHAR COMPUTER.
Daya daga cikin tambayoyin dajama’a suke yi a kowanelokaci shi ne ya mutum zai yi al-kacindayarasa kayan da yaajiye a cikin memory SD Card nawayarsa, Camera a sanadiyar kankare memory (formatting) kokuma an goge abin da ke ciki (deleting). Amma kafin in fadi yadda ake yin wannan aiki ko kuma manhajoji (software) da ake bukata yana da kyau in sanar da jama’a yadda shi wannan memory yake da kuma yadda ake lura da shi. Memory dai wani irin mazubi ne da aka yi shi domin ya ba mutum damar ya iya yin ajiyar kayan da aka yi su da wutar lantarki (electronic data) wanda ya hada da hotuna da rubutu da surkulle da duk wani abu da ake iya adana shi a cikin computer. Wadannan memory yana da yanayi mabanbanta dangane da yadda ake yin sa da kuma tsarin yinsa, sai dai mafi shahara shine wanda ake yin amfani da shi amafi yawan wayoyin tafida gidanka na zamani.
A baya, mafi yawan kanfanonin dasuke kirkirar wayoyi ko kamara kowa na yin irin nasa memory, dangane da girma ko fadi, wanda ya sanya akwai matsalasosai yadda memorin wani kamfani baya aiki a wata na’ura da ba tasa ba.
Amma bayan da waya kirar Android ta samu karbuwa sosai aduniya sai ya zama sun sami hadin
kai wurin tabbatar da mazubin memory ya zama yana darami iri daya wanda zaizama kowace waya ko tablet zata yi amfani da su.
A baya wannan memory ya na da tsada matuka, ga shi kuma yana da wahalar samuwa a kasash-en
mu, ga shi kuma ba shi da girman wurin kwasan bayanai, amma Alhamudu Lillahi a yanzu wannan ta kau domin ana samu memory wanda a kalla yana iya daukar Gig dubu shi kadai. Daga cikin abin da yake damun jama’a shi ne yawan lalacewarsa da kuma rashin sa’a wuringogewar abin da ke ciki. Mutane da dama suna manta cewar Memory shima kayan kwam-futa ne, kuma yana iya lalacewa kowane lokaci, musamman idan aka yi rashin sa’awanda yake rike da shi bai
iya lura da shi.
Wani lokaci ba wai memorin ya lalaceba ne, a a an sami matsala ne da inda aka saka shi. Misali zai iya yuwuwa ka sami wayar da take daukar memory dayake da tsarin ajiyar bayanaina FAT (File Allocated Table) to idanka saka shi a cikin wata wayar da baya daukar wannan tsarin sai ka ji ta fada maka cewar wannan memorin yayi dameji. Ko kuma wani lokaci zaka ga duk abin da ke cikn memorin ya ki budewa ko kuma ya nuna alamar lalacewa wanda wannan shima ba yana nuna cewar memorin ya daina aiki ba ne kokuma kayan cikinsa sun lalace. Shima wannan yana dadanganta ne da irin File Sysmem din da aka ajiye kayan tunfarko.
Wani lokaci kuma zaka ga ka dauko kaya daga cikin kwamfuta ko wata wayar amma da zarar ka tashi budewa sai ka ji ya nafada maka cewar Unsupported format wannan shima ba yana nu-fin cewar memorin ya lalace ba ne yana maganar cewar wayar bata da application din da zai bude.
To duk wadannan ba abin da za mu yi magana ba ne a kai. Muna son muyi magana ne ga mu-tum
da cikin rashin sani ko ma ganganci ya goge abin da ke cikin memory na wayarsa kuma yana son ya sake dawo da wannan kaya.
A tsari irin na bature da kuma yadda yayi kayan ajiya na kwamfuta wato storage devices yana
da kyau jama’a su sani cewar duk abin da ya taba shiga cikin memory na kwamfuta kowaya ko flash har abada yana nan, koda kuma an goge shi ko an yi formatin lallai yana nan, kumaza a iya dawo da shi. Saidai inda gizo ke saka shi ne dame yakamata in yi amfani wurindawo da wadannan kayan?
Akwai hanyoyi mabanbanta da jama’a suke yin amfani da su wurin dawo da kayan da suke ci-kin
memory, kadan daga ciki shine ta yin amfani da shafukan intanet domin samun biyan bukata. Sai dai a nawa shawarar ban cika son jama’a suna yin amfani da wasu shafukan intanet wurin irin wannan aiki ba, kasancewar mafi yawan irin wadannan shafuka na yan yaudara ne da zam-ba da kuma zubawa mutane miyagun virus cikin wayarka ko kuma kwamfutar ka.
Amma akwai na kirki saidai mafi yawansu sai ka biya kudi. A wannan karatun zan nuna mana
wadansu manhajojin kwamfuta na kyauta kuma garanti gaduk wanda yake son yayi amfani da su wurin dawo da kayan dasuka bace a memorinsa.
Idan memorin yana cikin waya ne kokuma cikin kamara kuma idan ka hada shi da kwamfuta baya
nuna memorin to yana dakyau ka ciro memorin daga cikin inda ya ke ka saka shi a cikinCard Reader domin fara yin wannan aiki.
Abin kiyayewa shi ne, tunda dakwamfuta zaka yi wannan gyara to ka sani mafi yawan kwam-futar da muke amfani da ita a wannan kasa ta mu kashi 60 suna dauke da virus mai cinye kayan kwamfita ma mayar da su shortcut, to, amfani da irin wannan kwamfutar akwai hatsari, saboda haka ka sami
kwamfutar da ka san tana da anti-virus mai kyau, kuma ana updating dinsa kafin ka zura shi.
Wani hanzari ba gudu ba, idan kasan akwai wadansu kaya acikin memori din to yana da kyau ka
kwashe su ka zuba su acikin wani folder domin kada garin so ka dawo da baya ya zama suna da suna iri daya da wannan sai ya daura a kansa.
Wadannan dai sune kadan daga cikin abin da zan iya janhankali a kai kafin in nuna mana soft-ware din da zan yimagana a kai. Amfani da wadannan application ba wani wahala ya ke da su ba, da farko dai dukkansu kyauta ne kuma suna yin aiki sai kamar yadda ya kamata duk da de ba wai zan fadi mataki bayan mataki bin kowane daya daga cikin su ba ne, sai dai zan fadi shi application din dakuma amfanin sa.1 Recuva (Na aiki a Windows ne kawai) Wannan applica-tion na Recuva(version 1.5) nauyin sa 4.02MB ne kuma kyauta ne, yana aiki a kwamfutar da take da operating system na Windows ana kuma iya saka shi a Windows 2000 zuwa sama. Idan kana son ka dawo da files din ka dake cikin memory din ka. Zaka saka memorin a cikin Card Reader sannan ka zura shi a cikin kwamfutar da ka yi installing wannan application na Recuva, sai ka tashe shi (recuva) sai
ka zabi shi memori din acikin jerin manyan kwakwalen da suke jikin kwamfutar. Sannansai ka taba maballin Scan.Zaka bashi lokaci don zai dawo dakayan da aka goge a cikinsannan zai baka maballin da aka rubuta Recover sai ka taba shi domin ya dawo maka da wanda kakeso.2 Pando-ra Recovery (Na aiki a
Windows ne kawai)Pandora Recovery shi ma kyauta ne yana da girman 3.12MB,yana aiki a kwamfutar da aka sa mata Windows kuma wacce Operating System dinta ya fara da Windows XP zuwa sama.
Shima yana aiki ne kamar yadda recuva, wato za a ciro memorin a saka a cikin Card Reader sai a saka a cikin kwamfutar da akayi Installing Pandora Recovery.Sannan zai zabi kodai yayiQuick Scan ko Deep Scan. Shi na Quick Scan ga wanda ya keson ya dawo da abubuwan ya-yi deleting ne amma wanda yake son ya dawo da wadanda aka yi formatting shi zai amfani da Deep Scan.Bayan ya gama scanning za ka iyazaba tsakanin kodai ka yi amfani da Pandora Re-covery Wizard sai ka yi amfani da sharudda da zai rika fitowa kana zaba har ka gama, ko kuma ka yi right click ka zabi abin da kake son ka dawo da su.
This post is copyright from fasahar internet 'kimiyya'
Recent Post
WHAT'S THE WEAKNESS/STRONGEST OF DXY
Today, February 19, 2026, the US Dollar Index (DXY) is actually displaying short-term strength, trading near a two-week high around the 97....






0 comments:
Post a Comment