BARKA DA ZUWA MAKARANTAR KOYON COMPUTER ACIKIN HARSHEN HAUSA DA KUMA YADDA FASAHA TAKE GUDANA ACIKIN DUNIYAR INTERNET. karka manta da following comment dakuma tambaya.

HOME

Sunday, May 15, 2022

AMFANIN GMAIL ACCOUNT (4.0)

Cigaba...
Yadda You Tube TV yake!
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡
YouTube TV tana daya daga cikin masu biyan kuɗi na hakika,sannan idan kabude tv kana samun damammaki kamar haka:
  • Kamallaki gidan TV kai tsaye daga manyan cibiyoyin watsa shirye-shirye.
  • Kanada Sararin DVR mara iyaka.
  • Kanada Shahararriyar USB tareda manyan cibiyoyin sadarwa.
ABUBUWAN DA YAKAMATA KASANI KAFIN KABUDE TV A YOUTUBE. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
Abubuwan daya kamata ka sani kafin kabude Gidan Talabijin na YouTube;
  • Zakana biyan dalar amurka sittin da hudu da dugo casa'in da taraa ($64.99) a matsayin haraji a wata.
  • Lokacin da kayi rijistar YouTube TV, za a tambaye ka lambar home zipcode/postalcode.
  • Hakanan za a iya tambayarka tabbacin inda kake ta hanyar neman izinin na'urarka. Yin hakan zai tabbatar da samun ingantattun hanyoyin sadarwa na gida.
  • Sababbin shiga wadanda sukayi rijista, suna samun sama da tashoshi 85 da aka bayar a cikin Tsarin Base a karan farko.
  • Hakanan zaka iya yin rijista da hanyoyin sadarwa,irinsu HBO Max,sannan kuma kazama daya daga cikin membobin youtube tv.
  • Yayin dakai rijista, youtube tv zai cajeka kuɗi kadan, Cibiyar ajiyar kuɗin ka zata sami Sakon neman izinin mu,amala da youtube tv saboda tabbatar da cewa katin kiredit dinka ka yana aiki ko a,a, kuma zasu iya ganin kuɗin dake cikin asusunka.
  • Za a cire dala 64.99 automatik da zarar sun tabbatar da katin yana aiki (cibiyar ajiyar kuɗin ka na iya tantance lokacin da wannan aikin zai faru).
  • YouTube TV baya karbar prepaid card saidai credit card.
YADDA AKE BUDE YOUTUBE TV ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
    Mataki na farko (rijista a manhajar you tube tv)
  1. Kaje rumbun adana manhajoji na playstore kasauke manhajar You Tube Tv.
  2. Saika budeshi kadanna maballin (begin the free trial)
  3. Saika shigar da bayananka na gmail account.
  4. Mataki na biyu (tabbatar da adireshin ka)
  5. zasu tambayeka Home-Zipcode katabbata kasaka daidai.
  6. zasu nemi izini daga na'urar ka cewa tarika nuna musu hakikanin inda kake (gps).
  7. Mataki na uku (zabar kungiya)
  8. kaduba You Tube (Base-plan) zakaga farashin kungiyar ka (membership).
  9. saika danna Next domin zuwa mataki nagaba, sannan kasa hadin Base-plan tahanyar danna da'ira (circle).
  10. saika danna Next idan ka tabbatar da abinda kazaba,saika tabbatar da katin kiredit dainka wanda zakai amfani dashi wajan biya kungiyar ka (membership).
  11. saika danna (BUY) domin kammalawa.
  12. Idan kuma kanadashi saika danna (already a member) sai kasaka bayananka. Ku Dakaci Fita Ta Gaba...
🔚
©️M.I.HARUNA
Share:

AMFANIN GMAIL ACCOUNT (3.0)

MANHAJAR YOUTUBE

Cigaba...
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡
    4. YOU TUBE: Manhajar youtube dandali ne da ake sada zumunci musamman ta hanyar hoto mai motsi (video), rumbun hoto mai motsi na youtube wanda yake a Amerika a hedkwatar san bruno dake kalfoniya, an kaddamar dashi a 14 ga watan fabrairu (2) shekara ta dubu biyu da biyar (2005) mallakin kamfanin google ne yanada mabiya sama da biliyan biyu (2billion), kana iya mallakar asusu aciki, tahanyar gmail kadai ake iya yin rijista domin samun damar subscribe, Like, Dislike, amma kowa da kowa na iya kallon bidiyo basai lallai kana da asusu ba, Sannan kana iya samun kudi a youtube tahanyar bude shago wato youtube channel, kana iya budewa ne kadai idan kamallaki gmail account.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
YADDA AKE BUDE YOUTUBE CHANNEL
Dafarko idan kashiga manhajar youtube saika latsa maballin dama daga sama,zakaga inda zaka saka email address da kuma password bayan kagama zakaga maballin yacanza zuwa farkon harafin sunanka,idan kuma kasa hoto a gmail dinka hoton ne zai bayyana, . karanta yadda ake saka hoto a profile na gmail Saika kara dannashi zaikaika wani shafi,kadanna inda kaga (create channel), idan yabude zaibaka dama ka kirkiri sabon channel naka, sai kasaka mata suna da bayanin abinda ta kunsa , shikenan ka kammala kirkirar tashar youtube mallakinka saika fara dora bidiyo. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
YADDA AKE DORA BIDIYO A YOU TUBE CHANNEL.
Tunda ka kammala kirkirar channel din sai kuma ka fara dora bidiyo, kaje rumbun adana manhajoji na playstore kadauko #Youtube studio, dashi ake amfani wajan sakawa channel bidiyo idan kabudeshi kai sign-in zakaga inda aka rubuta upload saika danna zaikaika ma,adanar bidiyon dake cikin wayarka kazabi Wanda kake so zaifara uploading bayan yagama zaka rubuta Abinda bidiyon ya kunsa dakuma bayanin jan hankalin mutane zuwaga kallon bidiyon. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
YADDA AKE SAMUN KUDI A YOU TUBE.
idan subscribers dinka suka kai dubu daya (1000) sannan kuma kana samun makallata (viewers)sosai to kamfanin google zasu saka tallace-tallace a farkon bidiyon dakake dorawa ,sai su fara biyanka kudade. Muhadu a fita tagaba inda zamuyi bayani akan #YouTube TV.
©️M.I.HARUNA.
Share:

YADDA AKE SAKA HOTO A PROFILE NA GMAIL

YADDA AKE SAKA HOTO A PROFILE NA GMAIL
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
Dayawa daga cikin mutane sunada ra,ayin sanya hoto a asusun su na kafafen sada zumunta Saboda duk wanda yasansu da yaga hotonsu zai ganesu Har yai musu magana, saboda suuna baicika tabbatar da mutum ba sai an hada da hoto, kasancewar akwai masu amfani da irin wannan suunan masu tarin yawa amma hotan mutum kadai ne zai iya tantanceshi kaiwaye, To ga yadda zaka sanya hotonka a gmail acount dinka cikin sauki;
  1. kashiga manhajar gmail din ko kuma ta manhajar lilo-lilo ta chrome,
  2. A bangaren dama daga sama kadanna alamar Harafin farko na sunanka wanda shike wakiltar asusunka,idan kuma canzawa zakayi to hoton naka zakagani,
  3. Bayan yabude sai kadanna inda kaga (Manage your google account)
  4. A bangaren hagu kadanna inda kaga (personal info.)
  5. bayan yabude saika danna inda kaga alamar harafin farko na sunanka, idan kuma canzawa zakai saika danna hotonka,
  6. zai kaika cikin ma,adanar wayarka saika zabi hoton da kakeso,
  7. saika yanke inda bakaso yafito acikin hoton ko kuma kabarshi haka, saika danna inda kaga ( set as profile photo.
  8. Shikenan kagama.
    🔚
    ©️M.I.HARUNA
Share:

Recent Post

WHAT'S THE WEAKNESS/STRONGEST OF DXY

 Today, February 19, 2026, the US Dollar Index (DXY) is actually displaying short-term strength, trading near a two-week high around the 97....

FOREX TRADING NEWS