Cigaba...
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡
-
4. YOU TUBE: Manhajar youtube dandali ne da ake sada zumunci musamman ta hanyar hoto mai motsi (video), rumbun hoto mai motsi na youtube wanda yake a Amerika a hedkwatar san bruno dake kalfoniya, an kaddamar dashi a 14 ga watan fabrairu (2) shekara ta dubu biyu da biyar (2005) mallakin kamfanin google ne yanada mabiya sama da biliyan biyu (2billion), kana iya mallakar asusu aciki, tahanyar gmail kadai ake iya yin rijista domin samun damar subscribe, Like, Dislike, amma kowa da kowa na iya kallon bidiyo basai lallai kana da asusu ba,
Sannan kana iya samun kudi a youtube tahanyar bude shago wato youtube channel, kana iya budewa ne kadai idan kamallaki gmail account.
YADDA AKE BUDE YOUTUBE CHANNEL
Dafarko idan kashiga manhajar youtube saika latsa maballin dama daga sama,zakaga inda zaka saka email address da kuma password bayan kagama zakaga maballin yacanza zuwa farkon harafin sunanka,idan kuma kasa hoto a gmail dinka hoton ne zai bayyana, . karanta yadda ake saka hoto a profile na gmail Saika kara dannashi zaikaika wani shafi,kadanna inda kaga (create channel), idan yabude zaibaka dama ka kirkiri sabon channel naka, sai kasaka mata suna da bayanin abinda ta kunsa , shikenan ka kammala kirkirar tashar youtube mallakinka saika fara dora bidiyo. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
YADDA AKE DORA BIDIYO A YOU TUBE CHANNEL.
Tunda ka kammala kirkirar channel din sai kuma ka fara dora bidiyo, kaje rumbun adana manhajoji na playstore kadauko #Youtube studio, dashi ake amfani wajan sakawa channel bidiyo idan kabudeshi kai sign-in zakaga inda aka rubuta upload saika danna zaikaika ma,adanar bidiyon dake cikin wayarka kazabi Wanda kake so zaifara uploading bayan yagama zaka rubuta Abinda bidiyon ya kunsa dakuma bayanin jan hankalin mutane zuwaga kallon bidiyon. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
YADDA AKE SAMUN KUDI A YOU TUBE.
idan subscribers dinka suka kai dubu daya (1000) sannan kuma kana samun makallata (viewers)sosai to kamfanin google zasu saka tallace-tallace a farkon bidiyon dakake dorawa ,sai su fara biyanka kudade. Muhadu a fita tagaba inda zamuyi bayani akan #YouTube TV.
©️M.I.HARUNA.






0 comments:
Post a Comment