YouTube TV tana daya daga cikin masu biyan kuɗi na hakika,sannan idan kabude tv kana samun damammaki kamar haka:
- Kamallaki gidan TV kai tsaye daga manyan cibiyoyin watsa shirye-shirye.
- Kanada Sararin DVR mara iyaka.
- Kanada Shahararriyar USB tareda manyan cibiyoyin sadarwa.
Abubuwan daya kamata ka sani kafin kabude Gidan Talabijin na YouTube;
- Zakana biyan dalar amurka sittin da hudu da dugo casa'in da taraa ($64.99) a matsayin haraji a wata.
- Lokacin da kayi rijistar YouTube TV, za a tambaye ka lambar home zipcode/postalcode.
- Hakanan za a iya tambayarka tabbacin inda kake ta hanyar neman izinin na'urarka. Yin hakan zai tabbatar da samun ingantattun hanyoyin sadarwa na gida.
- Sababbin shiga wadanda sukayi rijista, suna samun sama da tashoshi 85 da aka bayar a cikin Tsarin Base a karan farko.
- Hakanan zaka iya yin rijista da hanyoyin sadarwa,irinsu HBO Max,sannan kuma kazama daya daga cikin membobin youtube tv.
- Yayin dakai rijista, youtube tv zai cajeka kuɗi kadan, Cibiyar ajiyar kuɗin ka zata sami Sakon neman izinin mu,amala da youtube tv saboda tabbatar da cewa katin kiredit dinka ka yana aiki ko a,a, kuma zasu iya ganin kuɗin dake cikin asusunka.
- Za a cire dala 64.99 automatik da zarar sun tabbatar da katin yana aiki (cibiyar ajiyar kuɗin ka na iya tantance lokacin da wannan aikin zai faru).
- YouTube TV baya karbar prepaid card saidai credit card.
-
Mataki na farko (rijista a manhajar you tube tv)
- Kaje rumbun adana manhajoji na playstore kasauke manhajar You Tube Tv.
- Saika budeshi kadanna maballin (begin the free trial)
- Saika shigar da bayananka na gmail account. Mataki na biyu (tabbatar da adireshin ka)
- zasu tambayeka Home-Zipcode katabbata kasaka daidai.
- zasu nemi izini daga na'urar ka cewa tarika nuna musu hakikanin inda kake (gps). Mataki na uku (zabar kungiya)
- kaduba You Tube (Base-plan) zakaga farashin kungiyar ka (membership).
- saika danna Next domin zuwa mataki nagaba, sannan kasa hadin Base-plan tahanyar danna da'ira (circle).
- saika danna Next idan ka tabbatar da abinda kazaba,saika tabbatar da katin kiredit dainka wanda zakai amfani dashi wajan biya kungiyar ka (membership).
- saika danna (BUY) domin kammalawa. Idan kuma kanadashi saika danna (already a member) sai kasaka bayananka. Ku Dakaci Fita Ta Gaba...
©️M.I.HARUNA






0 comments:
Post a Comment