BARKA DA ZUWA MAKARANTAR KOYON COMPUTER ACIKIN HARSHEN HAUSA DA KUMA YADDA FASAHA TAKE GUDANA ACIKIN DUNIYAR INTERNET. karka manta da following comment dakuma tambaya.

HOME

Thursday, September 22, 2022

YADDA ZAKA SAMU KUDI A ONLINE (2.0)

↪️BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM↩️
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
(UPWORK)
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Upwork global Inc. Shine cikakken sunanshi sannan dandamalin aikinkai ne dake amurka  wanda yakeda hedkwata a Santa clara da San Francisco acikin California.
Ankafa kamfanin a shekarar dubu biyu da goma sha uku (2013) da sunan Elance-oDesk bayan hadewar kamfanin Elance Inc da kuma oDesk corp,
Wanda daga baya aka sauya mai suna zuwa Upwork a shekarar dubu biyu da goma sha biyar(2015).
A shekarar dubu biyu da goma sha bakwai (2017) Upwork nada mabiya miliyan shabiyu (12m) a matsayin masu aikin kai, dakuma mutum miliyan biyar (5m) amatsayin masu bada kwangila.
Wannan kenan...
↪️ zaka iya amfani da wannan dandamali kaima domin kasamu kudi to amma tayaya?↩️
Sai ka bude asusu amatsayin ma,aikaci (freelancer).
1. Dafarko kaje rumbun adana manhajoji na google playstore domin kasauke manhajar su,
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.upwork.android.apps.main&hl=en&gl=US&referrer=utm_source%3Dgoogle%26utm_medium%3Dorganic%26utm_term%3Dupwork
2. Ko kuma kashiga manhajar lilo-lilo (browser) chrome,safari,mozilla firefox,internet explorer,windows edge,vidmate,operamini,phoniex, dss.
3. Karubuta www.upwork.com saika shiga bayan yabude saika danna login.
4. Bayan yabude daga kasa zakaga inda aka rubuta sign up saika shiga zasu nunamaka cewa wanne irin asusu zaka bude? freelancer ko client, saika zabi freelancer kacike bayanan dasuka bukata.
5. Bayan kagama zaka tabbatar da haduwar email dinka da asusunka (email verification) tahanyar shiga email din kadanna rariyar likau din da suka tura maka (verification Link).
Shikenan kagama bude asusu, sannan kuma zaka amsa wasu tambayoyi wadanda dasune zasu amfani wajen fahimtar ra,ayinka.
Zasu binciki asusunka hadeda bayanan daka bayar acikin awa ashirin da hudu (24hrs) bayan sun tabbatar baka da wata matsala sai su budemaka kafara aiki.
↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️
Hanyoyin da zaka samu kudi
⬇️⬇️⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
️1. Dafarko kazama mai gaskiya sannan kabi dokar kamfani,kuma komai zakayi kayishi a bude, kudaden da kake samu hadeda kalar aikin dakake da wajen da za,a sameka misali social media handle,sannan zaka fadi nawa kake caji a aikinka amma kaduba masu irin aikinka nawa suke caji kafin kasa naka dan kada kai tsada.
2. Saika zabi tsarin da zai  dace dakai amatsayinka na ma,aikaci (freelancer)
A. Basic:- wannan tsarin kyautane amma domin haduwa da wanda zaibaka kwangila da tattaunawa tsakaninku, saikabiya wasu kudi, digo shabiyar na dalar amurka(US $0.15), zaka iya haduwa da sama da mutum dari da arba'in (140) a wata,sannan dole karika yawan sabunta samfur na  aikinka wanda yake zama kamar talla,tahaka ne mutane zasu rika zuwa.
B. Plus:- a wannan tsarin zakake biyan dalar amurka goma shahudu da digo cas'in da tara ($14.99) a wata amma yana dauke da duk abinda Basic kedashi tare da karin wadannan abubuwan.
a. Haduwa da mutum saba'in a wata(70per month).
b. Zaka shiga daya daga cikin wadanda ake biyansu kudin aikin su da tsada.
c. Za,a baka damar boye adadin kudin da kake samu.
d. Za,a baka damar canza addreshinka na yanar gizon dake asusunka (URL).
e. Bazasu rufemaka asusu ba dan ka dade baka shigaba.
f. Zaka hadu da abokan aiki nagartattu.
3. Gwajin inganci (rating)
Duk wanda kayiwa aiki yaji dadi zai danna maka tauraro a wajen gwajin inganci wanda yana farawa daga daya (*) zuwa biyar (*****)
Yana matukar taimakawa ma,aikaci domin duk wanda yaga kanada taurari to yasan tsohon hannune kai wato kasan aikinka angwadaka angani,sannan akwai percentage dayake nuna adadin aikin da kayi shima yana jawo hankalin wanda zaibaka aiki.
↪️Ayyukan da zaka iya yi a upwork↩️

1. Data Entry Specialists
2. Video Editors
3. Data Analyst
4. Shopify Developer
5. Ruby on Rails
6. Developer
7. Android Developer
8. Bookkeeper
9. Content Writer
10. Copywriter
11. Database
12. Administrator
13. Data Scientist
14. Front-End Developer
15. Game Developer
16. Graphic Designer
17. iOS Developer
18. Java Developer
19. JavaScript Developer
20. Logo Designer
21. Mobile App Developer
22. PHP Developer
23. Python Developer
24. Resume Writer
25. SEO Expert
26. Social Media Manager
27. Software Developer
28. Software Engineer
29. Technical Writer
30. UI Designer
31. UX Designer
Virtual Assistant
32. Web Designer
33. Wordpress Developer.
Akwai haraji dasuke dauka daga kudin daka samu, adadin kudin daka samu araba da lokacin daka dauka kana aikin (total amount of fee over time)
To kaga yawan aikinka karancin harajin dazasu dauka, misali
Zasu dauki kaso ashirin acikin dala daribiyar daka samu wanda shine mafi karancin kudin dazaka iya cirewa ta www.paypal.com (20%/$500)
(10%/$500.01)
(5%/$10,000)
Yadda zaka cire kudinka bayan kayi aiki an biyaka.
↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️
Upwork suna biyan kudi ta asusun paypal,duk sati suke tattara kudaden daka samu acikin wallet dinka su turamaka.
Idan baka dashi kucigaba da bibiyata domin sanin yadda zaka bude.
ALLAH yabada sa,a.
🔚
©️M.I.HARUNA
Share:

0 comments:

Recent Post

WHAT'S THE WEAKNESS/STRONGEST OF DXY

 Today, February 19, 2026, the US Dollar Index (DXY) is actually displaying short-term strength, trading near a two-week high around the 97....

FOREX TRADING NEWS