Monday, December 26, 2022
MENE NE FASAHAR ARTIFICIAL INTELLIGENCE(A.I)
➡Amincin Allah yatabbata agareku⬅
Ayau idan Allah yaso ya yarda zamuyi bayanine akan Fasahar A.I (artificial intelligence)wato kwaikwayon zubin dabi,ar dan adam.
Duniyar fasaha na kara cigaba, kasancewar kullum bincike akeyi anata kara tsatsubar sababbin fasahohi,
➡➡➡➡➡➡➡➡➡➡➡➡
Mene ne tsarin fasahar A.I?
tsarin fasahar a.i tsarine da aka sanyawa na,ura mai kwakwalwa domin takeyin tinani dakanta dakuma koyon abu dakanta (marchine learning) batare da ankoya mataba,sannan tana gudanar da abubuwa kamar dan adam ta sigar musayar bayanai,zakuyi hira da ita,zata baka shawara.
Misalan fasahar A.I
1. robot wato sakago; mutummutumi shima ansanya masa wannan fasahar tayadda zakuyi hira dashi kamar ,mutum kuma yanayin tinani sannan zai aiwatar da komai da kansa.
2. manhajar bincike ta GPT(chat.openai) wadda aka kirkira kwanannan da ta kerewa manhajar bincike ta google saboda ita zata baka amsane kai tsaye amma google zata baka inda akai rubutu akan abinda yashafi tambayarka ne,
3.Self driving car (mota mai tuka kanta) kawai saidai ka leka kaga steering na juyawa amma babu kowa aciki,ansanya mata tsarin tasan cewa tashiga cunkoso ko kuma ita kadai ke tafiya zata gane cewa tazo traffic ta tsaya idan kuma tabada hannu tagane ta tafi,
4. Manhajar da zata taimaka maka wajen wasu ayyukan na yau da kullum kamar kasuwanci,ta lissafa maka adadin kayan daka sayar da ribar daka ci da sauran wasu ayyukan daka sa taimaka,
5. Gida mai gudanar da kanshi ; wanna gida da abin mamakin yake domin idan kadawo daga wajen aiki ko kasuwa zaka shiga magana kawai zakaimasa yabude kaiwa bulb magana yakawo haske,kakira abinci daga kitchen yazo dining.
↘↘↘↘↘↘↘↘↘↘⬇↘
Rabe-Raben Fasahar A.I
⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
1.Artificial Intelligence (AI) ― wannan nau'i yana bayani akan shi din kansa fasahar (AI), watau fasahar na'urar mai kwakwalwa wacce aka ginata abisa son ta kwaikwayi ayyukan da kwakwalwar Dan-Adam take yi watau ‘Dabi'a’ kamar tunani, nazari, da sauransu.
2. Artificial General Intelligence (AGI) wannan kuma so ake AGI ya kasance ya fi AI ta yadda za'a daidaita fasahar da yin abu sak irin na Dan-Adam, watau duk wani abun da mutum zai iya yi na dabi'arsa - to fasahar AGI zata iya yi.
3. Artificial Super Intelligence (ASI) ― Wannan nau'i mai abun mamaki kenan. Watau ita fa wannan so ake ta ma fi Dan-Adam din; so ake ta fi Dan-Adam duk wasu dabi'u da ka san Dan-Adam yana da su. Ana son ne ta yiwa Dan-Adam fintinkau a komai.
Sannu akan hankali zamu zo wajen.
©M.I.HARUNA
Thursday, September 22, 2022
YADDA ZAKA DAWO DA ASUSUN FACEBOOK BAYAN ANKWACESHI. (1.0)
↪BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM↩
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Dafarko kashiga google search engine wato manhajar matambayi baya bata tahanyar manhajar lilo-lilo (browser) ta chrome, mozilla firefox, internet explorer, safari, phoniex, operamini, uc browser, vidmate, windows edge. Duk dai wadda kake da ita, kashiga karubuta
1. compromise account report page, ko facebook hacked account page.
Kashiga bayan yabude saika shiga
1. my account is compromised
2. Zai nunamaka gurin bincike (search bar) saikarubuta username ko email ko nambar wayar da ka bude asusun facebook din dashi kadanna search.
3.0 bayan ya nemo asusunka acikin ma,adanar bayanan su zai nuna maka asusunnaka saika kashiga,bayan yabude saika rubuta kalmar sirrinka dakai amfani dasu wajen sanyawa asusunka tsaro lokacin daka bude (password). Kadanna (continuo)
4.0 saika zabi dalilin dayasa kake zargin ankwace asusunnaka, idan dalilan da suka rubuta babu wanda yai daidai da naka, saika rubuta naka dalilin wato kadanna (i dont see the right option on this list) zasu baka dama. Saika Kadanna continuo
5.0 bayan yakammala shiga asusunka zai nunamaka (Getstarted) wato kabashi dama ya bincika wannan dalilin yaga ko hakanne, bayan kadanna (Getstarted) zaifara bincikawa,bayan yagama saika danna continuo.
6.0 zaibaka dama karubuta sabon makullin sirri. Saika danna Next
Anan yakamata kazabi kalmar sirri mai karfi (strong password) wanda yake hada lambobi (123456789) da bakake (abcd...z) hadeda alamomi (*#"'!/+@=),dakuma manyan bakake(ABCD...Z) da kanana(abcd...z)
Yana matukar wahalar da masu kutse (hackers)su gano.
Shikenan facebook dinka yadawo amma duk hakan zai yiwune idan wanda yakwace facebook din bai canza lambar wayar daka budeba ko email.
Idan baiyiba akwai wata hanyar zamuyi bayani a makala ta gaba.
Saikuma kaje kasauke facebook din naka daga kan kowacce na,ura
Yadda zaka sauke facebook daga kan kowacce waya (Logout).
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
1. Dafarko kashiga setting idan kana amfani da manhajar facebook (facebook app) ko facebook mara nauyi (facebook lite), idan kuma da manhajar lilo-lilo ce (browser) saika shiga setting and privacy.
2. Saika shiga Password and security
3. Zakaga wani guri an rubuta (WHERE YOU'RE LOGGED IN)
Kasa dashi kadan zakaga sunan wayarka idan Manhajar facebook (Facebook app) ne ko karamar manhajar facebook (Facebook lite)idan kuma manhajar lilo-lilo ce ta (operamini) zakaga anrubuta Android, to kasa dashi kadan zakaga Active now,wato itace wayar dakake amfani da facebook din alokacin, saika shiga (See more) zakaga duk wayar daka taba saka facebook dinka akai, daga can kasa zakaga (Logout in all session) saika kashiga zaicireka daga kan kowacce waya sai (Active now)kadai zaibari.
🔚
©️M.I.HARUNA
YADDA ZAKA SAMU KUDI A ONLINE (2.0)
↪️BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM↩️
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
(UPWORK)
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Upwork global Inc. Shine cikakken sunanshi sannan dandamalin aikinkai ne dake amurka wanda yakeda hedkwata a Santa clara da San Francisco acikin California.
Ankafa kamfanin a shekarar dubu biyu da goma sha uku (2013) da sunan Elance-oDesk bayan hadewar kamfanin Elance Inc da kuma oDesk corp,
Wanda daga baya aka sauya mai suna zuwa Upwork a shekarar dubu biyu da goma sha biyar(2015).
A shekarar dubu biyu da goma sha bakwai (2017) Upwork nada mabiya miliyan shabiyu (12m) a matsayin masu aikin kai, dakuma mutum miliyan biyar (5m) amatsayin masu bada kwangila.
Wannan kenan...
↪️ zaka iya amfani da wannan dandamali kaima domin kasamu kudi to amma tayaya?↩️
Sai ka bude asusu amatsayin ma,aikaci (freelancer).
1. Dafarko kaje rumbun adana manhajoji na google playstore domin kasauke manhajar su,
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.upwork.android.apps.main&hl=en&gl=US&referrer=utm_source%3Dgoogle%26utm_medium%3Dorganic%26utm_term%3Dupwork
2. Ko kuma kashiga manhajar lilo-lilo (browser) chrome,safari,mozilla firefox,internet explorer,windows edge,vidmate,operamini,phoniex, dss.
3. Karubuta www.upwork.com saika shiga bayan yabude saika danna login.
4. Bayan yabude daga kasa zakaga inda aka rubuta sign up saika shiga zasu nunamaka cewa wanne irin asusu zaka bude? freelancer ko client, saika zabi freelancer kacike bayanan dasuka bukata.
5. Bayan kagama zaka tabbatar da haduwar email dinka da asusunka (email verification) tahanyar shiga email din kadanna rariyar likau din da suka tura maka (verification Link).
Shikenan kagama bude asusu, sannan kuma zaka amsa wasu tambayoyi wadanda dasune zasu amfani wajen fahimtar ra,ayinka.
Zasu binciki asusunka hadeda bayanan daka bayar acikin awa ashirin da hudu (24hrs) bayan sun tabbatar baka da wata matsala sai su budemaka kafara aiki.
↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️
Hanyoyin da zaka samu kudi
⬇️⬇️⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
️1. Dafarko kazama mai gaskiya sannan kabi dokar kamfani,kuma komai zakayi kayishi a bude, kudaden da kake samu hadeda kalar aikin dakake da wajen da za,a sameka misali social media handle,sannan zaka fadi nawa kake caji a aikinka amma kaduba masu irin aikinka nawa suke caji kafin kasa naka dan kada kai tsada.
2. Saika zabi tsarin da zai dace dakai amatsayinka na ma,aikaci (freelancer)
A. Basic:- wannan tsarin kyautane amma domin haduwa da wanda zaibaka kwangila da tattaunawa tsakaninku, saikabiya wasu kudi, digo shabiyar na dalar amurka(US $0.15), zaka iya haduwa da sama da mutum dari da arba'in (140) a wata,sannan dole karika yawan sabunta samfur na aikinka wanda yake zama kamar talla,tahaka ne mutane zasu rika zuwa.
B. Plus:- a wannan tsarin zakake biyan dalar amurka goma shahudu da digo cas'in da tara ($14.99) a wata amma yana dauke da duk abinda Basic kedashi tare da karin wadannan abubuwan.
a. Haduwa da mutum saba'in a wata(70per month).
b. Zaka shiga daya daga cikin wadanda ake biyansu kudin aikin su da tsada.
c. Za,a baka damar boye adadin kudin da kake samu.
d. Za,a baka damar canza addreshinka na yanar gizon dake asusunka (URL).
e. Bazasu rufemaka asusu ba dan ka dade baka shigaba.
f. Zaka hadu da abokan aiki nagartattu.
3. Gwajin inganci (rating)
Duk wanda kayiwa aiki yaji dadi zai danna maka tauraro a wajen gwajin inganci wanda yana farawa daga daya (*) zuwa biyar (*****)
Yana matukar taimakawa ma,aikaci domin duk wanda yaga kanada taurari to yasan tsohon hannune kai wato kasan aikinka angwadaka angani,sannan akwai percentage dayake nuna adadin aikin da kayi shima yana jawo hankalin wanda zaibaka aiki.
↪️Ayyukan da zaka iya yi a upwork↩️
1. Data Entry Specialists
2. Video Editors
3. Data Analyst
4. Shopify Developer
5. Ruby on Rails
6. Developer
7. Android Developer
8. Bookkeeper
9. Content Writer
10. Copywriter
11. Database
12. Administrator
13. Data Scientist
14. Front-End Developer
15. Game Developer
16. Graphic Designer
17. iOS Developer
18. Java Developer
19. JavaScript Developer
20. Logo Designer
21. Mobile App Developer
22. PHP Developer
23. Python Developer
24. Resume Writer
25. SEO Expert
26. Social Media Manager
27. Software Developer
28. Software Engineer
29. Technical Writer
30. UI Designer
31. UX Designer
Virtual Assistant
32. Web Designer
33. Wordpress Developer.
Akwai haraji dasuke dauka daga kudin daka samu, adadin kudin daka samu araba da lokacin daka dauka kana aikin (total amount of fee over time)
To kaga yawan aikinka karancin harajin dazasu dauka, misali
Zasu dauki kaso ashirin acikin dala daribiyar daka samu wanda shine mafi karancin kudin dazaka iya cirewa ta www.paypal.com (20%/$500)
(10%/$500.01)
(5%/$10,000)
Yadda zaka cire kudinka bayan kayi aiki an biyaka.
↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️↘️
Upwork suna biyan kudi ta asusun paypal,duk sati suke tattara kudaden daka samu acikin wallet dinka su turamaka.
Idan baka dashi kucigaba da bibiyata domin sanin yadda zaka bude.
ALLAH yabada sa,a.
🔚
©️M.I.HARUNA
Sunday, August 14, 2022
YADDA AKE SAMUN KUDI A YANAR GIZO-GIZO (1.0)
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Samun kudi a yanar gizo-gizo abune daya zama ruwan dare game duniya saidai anasamun bata gari da suke damfarar mutane shiyasa wasu har yanzu basu yadda da lamarin ba,
Amma babu yadda muka iya tunda muna cikin karni na ashirin ne wanda ake kira da (digital error) ko (computer edge) a turance,zamanine na komai yakoma kan na'ura mai kwakwalwa,haka zalika anmaida abubuwa da yawa badini wato E (electronically) kudi akwai na yanar gizo wato (digital currency) irinsu e-naira,pi coins,pin coins,SBpoins,bitcoins, yuan coins,o-coins, da sauransu.
Haka zalika ma,ajiyar kudi (bank) ankoma cashless policy, irinsu e-wallet,e-banking,paypal,gift card,palmpay,Opay, dasauransu.
Hanyoyin isar da sakonni ta hanyar kiran waya ko kiran mutum kana ganin shi yana ganinka (video call) wanda yan kan tsarin manhajoji masu yawa irinsu Duo na kamfanin google, Messenger na kamfanin facebook, whatsapp, Skype, Yahoo! Messenger.
Saikuma tsarin sakon e-mail wan yake sadarwa tsakanin na'urori (client) da (server) shima yana kan manhajoji masu tarin yawa irinsu facebook, whatsapp, instagram,twitter,we chat, eBuddy, snapchat, skype, Ayoba, tiktok, Gmail, hotmail, yahoo!,da sauransu, duk suna amfani da tsarin sakon lantarki ne na E.
Kasuwannin mu cike suke da barayi da masu yankan ajihu da masu maganin gargajiya na karya,kasha kaita zawo,duk da kasancewar hakan amma bamu dena zuwa ba,saidai mun dauki matakan da zai rage faruwar hakan.
Kasan cewar aiki a yanar gizo muradi ne daga cikin #MURADAN_KARNI shima hakanan zamu rungumeshi mukoyi rayuwa dashi musan masu gaskiyar ciki da kuma yan damfara,
Acikin amintattu wadanda suna biya dazarar ka kammala aikinka acikinsu akwai Swagbucks,
Swagbucks wani kamfanine wanda ake sayen kaya (shopping) da kuma bincike (search) gamida tambayoyin jin ra,ayi (survey).
Kuma idan kayi daya daga cikin wadannan abubuwan biyanka za,ayi,
Suna biya ne da SBpoint wanda SBpoints dari 100 yana daidai da dala $1, zasu biyaka tahanyar asusun paypal.
Akwai sauran bayanai kudaceni...
Ga link nan kuje kuyi rijista.
https://www.swagbucks.com/lp-savings-button?cmp=695&cxid=swagbuttonref&rb=126602958&extRefCmp=1&extRb=126602958.
©️M.I.HARUNA
Friday, June 10, 2022
YADDA ZAKA KARE KANKA DAGA HACKERS (3.0)
MUSTAPHA IBRAHIM HARUNAJune 10, 2022https://muradankarni.blogspot.com/2022/05/amfanin-gmail-account-30.html, https://muradankarni.blogspot.com/2022/05/amfanin-gmail-account-40.html
No comments
YADDA ZAKA KARE WHATSAPP DINKA DAGA HACKERS
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Bayan kammala bayani akan kakkarfan matakin tsaro da zakai amfani dashi wajen kare asusun #Facebook dinka wanda shine kololuwa domin babu sama dashi ayanzu, nan ma zanyi bayani akan tsaro mafi inganci da karfi dazakai amfani dashi wajen kare asusunka na #Whatsapp daga #Hackers,
(Two-step verification)
Ga yadda zakayi;
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
1. Bayan kashiga manhajar whatsapp dinka, kadanna wasu digo guda uku bangaren dama daga sama,
2. Saika shiga Settings
3. Saika danna Account
4. Saika shiga Two-step verification,
5. Saika danna Enable
6. Zai nuna maka inda zaka rubuta lambobin sirri (password/pin) guda shida,
7. Saikuma ka kara rubutawa domin tabbatar da manufarka (confirm pin)
8. Saikuma karubuta email dinka wanda dashine za,ai amfani, idan kamanta lambobin sirrin (forget password)
🔚
Shikenan ka kammala.
#Two_step_verification.
#Two_factor_authentication.
©️M.I.HARUNA
YADDA ZAKA KARE KANKA DAGA HACKERS (2.0)
YADDA ZAKA KARE FACEBOOK DINKA DAGA HACKERS
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️↕️
Mafi kololuwar tsaro wanda yafi kowanne, shine (Two-factor authentication)
Akanshi zamuyi bayani.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
1. Dafarko kashiga setting acikin manhajar facebook ko facebook lite,idan kuma browser ce saika shiga setting and privacy.
2. Sannan kashiga password and security
3. Sannan kadanna Use Two-factor authentication
4. Saikuma kashiga Use text message (sms).
5. Sai kasaka numbar wayarka wadda take aiki, saika danna continue.
6. Daga nan zasu tura maka lambobi guda shida(6) domin tabbatar dacewa lambar na aiki saika danna continue.
7. Two-factor authication yafara aiki, daga nan duk idan kayi login a wata wayar ko browser wadda baka taba login aciki ba, wato (unknown browser) to zasu tura maka lambobin tantancewa (verification code) guda takwas (8) idan kasaka sannan accoun din zai bude.
Kaga koda wani yasan password dinka bazai iya shigaba tunda bazai budeba saika saka lambobin da zasu tura maka alokacin wanda suke canzawa duk bayan minti daya.
Muhadu a #WHATSAPP
🔚
©️M.I.HARUNA
YADDA ZAKA KARE KANKA DAGA HACKERS (1.0)
YADDA ZAKA KARE FACEBOOK DINKA DAGA HACKERS. (1.0)
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️
Kasantuwar samun matasan hackers (upcoming hackers) yasa ake yawaita kutse acikin social media musamman facebook dayake da saukin mu,amala da farin jini,
Wasu daga cikin masu kutse cikin account din mutane, sunayine domin gwada ilimin da suka koya na hacking wato NETWORKING SKILLS wanda yahada da ilimin;
1. WEP versus WPS password
2. NAT
3. MAC Addresses
4. Routers
5. Ports
6. VPN
7. IPv6
8. DNS
9. Subnetting
10. DHCP
11. Private and public IPs
12. Ipv4
13. OSI Modelling
14. Packets
15. TCP/IP
Wasu kuma sunayine domin kasuwanci,
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Sukan duba mutumin da yake da abokai masu yawa domin suyi amfani da account dinsa suke tallace-tallace aciki, kamfanin da sukewa tallar yana biyansu.
Wasu kuma domin su aikata laifi,
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Sukanyi hakanne domin kada akamasu kaikuma kashiga hannu, kaga kataka sawun barawo kenan,shine kutse mafi muni, wani yayi amfani da zatinka ya aikata laifi, azo bincike akamaka bakaci nanin ba nanin tacika Allah ya sawwake.
Wasu kuma sunayine domin suyi damfara,
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
Zasuyi amfani da account dinka su rika turawa abokananka sako cewa kana neman taimako ataimaka maka da kudi ko katin kiran waya,
Amatsayin kaine tunda shidai ba ganinka yakeba,kaga bazai gane cewa bakaineba, kaga an zubar maka da mutunci.
Muhadu a fita tagaba domin sanin yadda zaka kare kanka daga yan #dandatsa
🔚
©️M.I.HARUNA
Sunday, May 15, 2022
AMFANIN GMAIL ACCOUNT (4.0)
Cigaba...
Yadda You Tube TV yake!
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡
YouTube TV tana daya daga cikin masu biyan kuÉ—i na hakika,sannan idan kabude tv kana samun damammaki kamar haka:
Abubuwan daya kamata ka sani kafin kabude Gidan Talabijin na YouTube;
©️M.I.HARUNA
YouTube TV tana daya daga cikin masu biyan kuÉ—i na hakika,sannan idan kabude tv kana samun damammaki kamar haka:
- Kamallaki gidan TV kai tsaye daga manyan cibiyoyin watsa shirye-shirye.
- Kanada Sararin DVR mara iyaka.
- Kanada Shahararriyar USB tareda manyan cibiyoyin sadarwa.
Abubuwan daya kamata ka sani kafin kabude Gidan Talabijin na YouTube;
- Zakana biyan dalar amurka sittin da hudu da dugo casa'in da taraa ($64.99) a matsayin haraji a wata.
- Lokacin da kayi rijistar YouTube TV, za a tambaye ka lambar home zipcode/postalcode.
- Hakanan za a iya tambayarka tabbacin inda kake ta hanyar neman izinin na'urarka. Yin hakan zai tabbatar da samun ingantattun hanyoyin sadarwa na gida.
- Sababbin shiga wadanda sukayi rijista, suna samun sama da tashoshi 85 da aka bayar a cikin Tsarin Base a karan farko.
- Hakanan zaka iya yin rijista da hanyoyin sadarwa,irinsu HBO Max,sannan kuma kazama daya daga cikin membobin youtube tv.
- Yayin dakai rijista, youtube tv zai cajeka kuÉ—i kadan, Cibiyar ajiyar kuÉ—in ka zata sami Sakon neman izinin mu,amala da youtube tv saboda tabbatar da cewa katin kiredit dinka ka yana aiki ko a,a, kuma zasu iya ganin kuÉ—in dake cikin asusunka.
- Za a cire dala 64.99 automatik da zarar sun tabbatar da katin yana aiki (cibiyar ajiyar kuÉ—in ka na iya tantance lokacin da wannan aikin zai faru).
- YouTube TV baya karbar prepaid card saidai credit card.
-
Mataki na farko (rijista a manhajar you tube tv)
- Kaje rumbun adana manhajoji na playstore kasauke manhajar You Tube Tv.
- Saika budeshi kadanna maballin (begin the free trial)
- Saika shigar da bayananka na gmail account. Mataki na biyu (tabbatar da adireshin ka)
- zasu tambayeka Home-Zipcode katabbata kasaka daidai.
- zasu nemi izini daga na'urar ka cewa tarika nuna musu hakikanin inda kake (gps). Mataki na uku (zabar kungiya)
- kaduba You Tube (Base-plan) zakaga farashin kungiyar ka (membership).
- saika danna Next domin zuwa mataki nagaba, sannan kasa hadin Base-plan tahanyar danna da'ira (circle).
- saika danna Next idan ka tabbatar da abinda kazaba,saika tabbatar da katin kiredit dainka wanda zakai amfani dashi wajan biya kungiyar ka (membership).
- saika danna (BUY) domin kammalawa. Idan kuma kanadashi saika danna (already a member) sai kasaka bayananka. Ku Dakaci Fita Ta Gaba...
©️M.I.HARUNA
AMFANIN GMAIL ACCOUNT (3.0)
Cigaba...
➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡️➡
-
4. YOU TUBE: Manhajar youtube dandali ne da ake sada zumunci musamman ta hanyar hoto mai motsi (video), rumbun hoto mai motsi na youtube wanda yake a Amerika a hedkwatar san bruno dake kalfoniya, an kaddamar dashi a 14 ga watan fabrairu (2) shekara ta dubu biyu da biyar (2005) mallakin kamfanin google ne yanada mabiya sama da biliyan biyu (2billion), kana iya mallakar asusu aciki, tahanyar gmail kadai ake iya yin rijista domin samun damar subscribe, Like, Dislike, amma kowa da kowa na iya kallon bidiyo basai lallai kana da asusu ba,
Sannan kana iya samun kudi a youtube tahanyar bude shago wato youtube channel, kana iya budewa ne kadai idan kamallaki gmail account.
YADDA AKE BUDE YOUTUBE CHANNEL
Dafarko idan kashiga manhajar youtube saika latsa maballin dama daga sama,zakaga inda zaka saka email address da kuma password bayan kagama zakaga maballin yacanza zuwa farkon harafin sunanka,idan kuma kasa hoto a gmail dinka hoton ne zai bayyana, . karanta yadda ake saka hoto a profile na gmail Saika kara dannashi zaikaika wani shafi,kadanna inda kaga (create channel), idan yabude zaibaka dama ka kirkiri sabon channel naka, sai kasaka mata suna da bayanin abinda ta kunsa , shikenan ka kammala kirkirar tashar youtube mallakinka saika fara dora bidiyo. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
YADDA AKE DORA BIDIYO A YOU TUBE CHANNEL.
Tunda ka kammala kirkirar channel din sai kuma ka fara dora bidiyo, kaje rumbun adana manhajoji na playstore kadauko #Youtube studio, dashi ake amfani wajan sakawa channel bidiyo idan kabudeshi kai sign-in zakaga inda aka rubuta upload saika danna zaikaika ma,adanar bidiyon dake cikin wayarka kazabi Wanda kake so zaifara uploading bayan yagama zaka rubuta Abinda bidiyon ya kunsa dakuma bayanin jan hankalin mutane zuwaga kallon bidiyon. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
YADDA AKE SAMUN KUDI A YOU TUBE.
idan subscribers dinka suka kai dubu daya (1000) sannan kuma kana samun makallata (viewers)sosai to kamfanin google zasu saka tallace-tallace a farkon bidiyon dakake dorawa ,sai su fara biyanka kudade. Muhadu a fita tagaba inda zamuyi bayani akan #YouTube TV.
©️M.I.HARUNA.
YADDA AKE SAKA HOTO A PROFILE NA GMAIL
YADDA AKE SAKA HOTO A PROFILE NA GMAIL
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
Dayawa daga cikin mutane sunada ra,ayin sanya hoto a asusun su na kafafen sada zumunta Saboda duk wanda yasansu da yaga hotonsu zai ganesu Har yai musu magana, saboda suuna baicika tabbatar da mutum ba sai an hada da hoto, kasancewar akwai masu amfani da irin wannan suunan masu tarin yawa amma hotan mutum kadai ne zai iya tantanceshi kaiwaye, To ga yadda zaka sanya hotonka a gmail acount dinka cikin sauki;
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇
Dayawa daga cikin mutane sunada ra,ayin sanya hoto a asusun su na kafafen sada zumunta Saboda duk wanda yasansu da yaga hotonsu zai ganesu Har yai musu magana, saboda suuna baicika tabbatar da mutum ba sai an hada da hoto, kasancewar akwai masu amfani da irin wannan suunan masu tarin yawa amma hotan mutum kadai ne zai iya tantanceshi kaiwaye, To ga yadda zaka sanya hotonka a gmail acount dinka cikin sauki;
- kashiga manhajar gmail din ko kuma ta manhajar lilo-lilo ta chrome,
- A bangaren dama daga sama kadanna alamar Harafin farko na sunanka wanda shike wakiltar asusunka,idan kuma canzawa zakayi to hoton naka zakagani,
- Bayan yabude sai kadanna inda kaga (Manage your google account)
- A bangaren hagu kadanna inda kaga (personal info.)
- bayan yabude saika danna inda kaga alamar harafin farko na sunanka, idan kuma canzawa zakai saika danna hotonka,
- zai kaika cikin ma,adanar wayarka saika zabi hoton da kakeso,
- saika yanke inda bakaso yafito acikin hoton ko kuma kabarshi haka, saika danna inda kaga ( set as profile photo. Shikenan kagama.
🔚
©️M.I.HARUNA
Friday, April 15, 2022
AMFANIN GMAIL ACCOUNT (2.0)
Cigaba...
A darasin daya gabata munyi bayani akan menene Gmail da kuma amfaninsa,to yanzu zamu cigaba;
- DUO: wata manhaja ce wadda kamfanin google suka gina saboda yin (video call) Wato yin kira kana ganin mutum yana ganin ka, domin cin moriyar hakan saika sauke Manhajar a rumbun manhajoji na google wato playstore, Kabude kayi register da lambar wayar ka, duk wanda yayi register acikin lambobin wayarka zaku hadu, haka zalika idan kasaka gmail dinka acikin computer tahanyar manhjar lilo-lilo ta chrome zaka iya video call da mutum wanda yake acikin contact dinka matukar yana online, zaka gane haka ne idan kaduba hagu daga kasa an rubuta chat idanka taba wajan zainuna maka wanda yake online da koriyar alama.
- COMPOSE MAIL: Kirkirar sako ko wasika dan turawa wani ko adanawa dan gaba, Kaduba sama daga hagu idan kadanna zai nuna maka wajan rubuta wasika, To: yana nufin wanda zaka turawa sakon, zaka iya rubutawa kuma zaka iya dakkowa cikin wadanda kake dasu daya ko sama da haka, amma idan sunfi daya zakake raba tsakanin su da comma ( , ) misali; miharuna3449@gmail.com,sulphuricacid3449@yahoo.com haka zakai konawa ne. MESSAGE: yana nufin sakon da zaka tura wato (message body), ATTACHEMENT: wato hada sakon da wani file, hoto ko documents, sai kuma SEND wato tura sakon kenan.
- MEETING: Ganawa tsakanin wasu mutane domin tattauna wasu muhimman batutuwa,a kamfani ko makaranta da sauran wurare, idan kashiga gmail ta manhajar lilo-lilo ta chrome kasa daga hagu zakaga an rubuta #meeting idan kadanna zai baka zabi biyu kodai ka kirkiri ganawar(meeting) kokuma ka amsa gayyatar ganawar ta hanyar rubuta wasu lambobin sirri da makirkirin ganawar yabaka.
Saturday, February 12, 2022
YADDA AKE ROOTING
YADDA AKE ROOTING Dafarko dai kawai ka antaya internet kaje kai searching din wannan apps din mai suna #king root bayan ka saukeshi saika shiga bayan yabude saika danna inda aka rubuta” root the phone” zaifara idan ya kammala zai cemaka “your phone has been rooted” sannan kadauko wannan apps din domin duba cewa ko wayar taka tayi rooting kadakko wanna apps din mai suna #root checker zai bincika maka wayarka idan anyi rooting ko a,a. (Tunatarwa) akwai apps dayawa nayin rootin wasu suna amfani da data wasu kuma basayi, ka dauko wanda yadace dakai idan baiyiba saika dakko version nagaba.
MENE NE AMFANIN ROOTING Amfanin rooting yana da yawa amma ga kadan daga ciki;
-
1. TWEAKING
2. Canzawa android version
3. Canzawa android animation
4. Karawa internal memory yawa
5. Amfani da manyan applications
6. Bude Hd Videos
AMFANIN GMAIL ACCOUNT (1.0)
Kasancewar yanzu muna karni na 21 wato zamanin kimiyya da fasaha wato (digital error) a turance zamanin da akeso amaida komai E wato (electronically) zuwa yanzu akwai E da yawa, e-money,e-learning,e-mail;e-motors,e-market; e-wallet,Da sauransu.
MENE NE E-MAIL? E-mail antakaicene cikakken abinda yake nufi shine electronic mail wato sakon lantarki wanda yake da matukar sauri yayin da aka aikashi.
BAN-BANCIN EMAIL DA SIMCARD E-mail baya da kaidar mu,amala wato duk inda katura shi zaije batare da wani sharadiba,amma simcard yana da kaida. Saurin isar da sako akkan lokaci ba tare da wata matsalaba, amma simcard akan samu matsala. Simcard baya bukatar damar shiga yanar gizo-gizo service+network sun wadatar amma email yana bukatar hadin shiga yanar gizo-gizo. Email yanada ma,ajiya wato (storage) mai yawa amma simcard baya da storage mai yawa. GMAIL Google mail cikakken abinda yake nufi kenan ayanzu shine email din da ake yayi kasancewar wasu basu san amfanin shiba yasa zanyi bayani game da abinda yashafi gmail account, Wata hanya ce da akke sadar da sakonni tsakanin na urori wanda kamfanin google ya kirkira yanada 15gb na adadin ma,ajiya (15gb storage), ana ajiye fayiloli (files) acikinsa kamar hotuna,hoto mai motsi (videos), lambobin kira (contacts); ma,ajiyar bayanai (documents) da sauransu. Gmail yanada masu amfani dashi kimanin biliyan daya da miliyan dari biyar(1.5 billion), ana shigar shi ne ta hanyar browser ko kuma manhajar gmail (gmail App),yana dauke da yaruka 105.
AMFANIN GMAIL ACCOUNT Amfanin e-mail abune mai fadi saidai adan tsakuro kawai ayi bayani Afanin gmail yashiga cikin wadannan manhajojin wadanda mallakin google ne, zanyi bayanin su daya bayan daya.
-
<>Video call (duo):
- Compose mail:
- Calender
- Chat:
- Meeting:
- YouTube:
- Blog:
- Photos:
- Chrome:
- Google play store:
- Drive
- Map
- News
- Form
- Contacts
- Google ads. Mu hadu a fita ta gaba.
Recent Post
WHAT'S THE WEAKNESS/STRONGEST OF DXY
Today, February 19, 2026, the US Dollar Index (DXY) is actually displaying short-term strength, trading near a two-week high around the 97....










